An kaiwa tankokin Nato hari a pakistan

Hari akan tankokin Nato

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun sake kaiwa tankunan dakarun kungiyar tsaro ta Nato a hari a Pakistan.

Harin ya yi sanadiyyar kone kimanin tankoki talatin da ke ajiye a gefen titi, daura da wani kantin sayar da abinci dake nisan kilomita dari, daga birnin Quetta a yammacin kasar.

Tankokin na dauke da fetur ne wanda za su kaiwa dakarun kungiyar tsaro ta Nato a kasar Afghanistan, wadda ke makwabtaka da Pakistan.

Tun a makon jiya ne dai 'yan kungiyar Taliban a kasar Pakistan ke kai irin wadannan hare-haren bayan da mahukunta suka rufe babbar hanyar shiga Afghanistan a sanadiyyar kashe sojin Pakistan da mayakan Nato suka yi.