Martanin Majalisar Dinkin Duniya a kan Sudan

Jakadun kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya sun bukaci mahukuntan kasar Sudan da su kara kokari wajen kare jami'an agaji da dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur da ke kasar.

Jakadu goma sha biyar din da ke ziyara a Darfur sun yi tur da sace wani jami'in rundunar kiyaye zaman lafiya ta hadin gwiwa, tsakanin majalisar dinkin duniya da gamayyar kasashen Afrika, dan asalin kasar Hungary.

Jagoran tawagar, jakadan Burtaniya a majalisar dinkin duniya, Mark Grant ya ce lamarin tsaron na kara tabarbarewa a kasar ta Sudan.

Ya kara da cewa a bana a samu karuwar tashe-tashen hankula wanda hakan bai yi musu dadi ba.

Ya bayyana sace wani jami'in majaliasar dinkin duniya duniya da aka yi ranar Alhamis din da ta gabata a garin El Fasher, a matsayin alamar karancin tsaro a kasar.