Ana ci gaba da murna a Chile

Ana ta murna a Chile
Image caption Ana ta murna a Chile

Ana ci gaba da murna a kasar Chile bayan nasarar da injiniyoyi suka yi ta kaiwa inda masu hakar ma'adinan nan su talatin da uku suke tun kimanin watanni biyun da suka gabata.

Ma'aikatan ceto da injiniyoyin da wakilan gwamnati da kuma iyalan mutanen sun yi ta murna suna rungumar juna saboda nasarar da aka samu.

Matar shugaban kasar Chilen, Cecilia Morel, ta nuna farin cikinta dangane da wannan sakamako.

“Tun daga ranar da abin ya faru gwamnati ta yanke shawarar ganin cewa ta ceto masu hakar ma'adinan kuma muna faricin cikin cewa sun rayu”.