'Nine shugaban Arewa', inji Namadi Sambo

Mataimakin Shugaban Najeriya, Namadi Sambo
Image caption Mataimakin Shugaban Najeriya, Namadi Sambo

Mataimakin Shugaban Najeriya, Architect Muhammad Namadi Sambo, ya bayyana cewa a siyasance shi ne shugaban arewacin kasar, don haka ikirarin da wadansu ke yi na shugabancin yankin yana ba shi mamaki.

Mataimakin shugaban ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC a Kaduna, inda ya kuma mayar da martani ga masu kira ga Shugaba Goodluck Jonathan ya yi murabus.

“Wadansu da suke magana—wannan ya fito ya ce shi ne shugaba na arewa—mu mamaki abin ya ke ba mu, amma ka san mu ba ma da surutai da yawa.

“Allah Ubangiji Ya gaya mana a matsayinmu na Musulmi—kai har ma Kirista—cewa shugabanci Allah ne Ya ke bayarwa a lokacin da Ya ga dama, kuma shi ne ya ke karba.

“A yau, ba shakka kowa ya sani, Allah Ubangiji Ya riga Ya sa ni, Architect Namadi Sambo, nine shugaba a siyasance a wannan sashe na kasar nan...”.

Dangane da kiran da wadansu dattawan arewa suka yi na Shugaba Goodluck ya sauka daga kan mukaminsa kuwa, Architect Namadi Sambo ya yi kira ne ga ’yan Najeriya “su daina sauraron maganganun da ba za su kai mu gaci ba”.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana ra'ayin sa a kan nacewar da wasu ‘yan arewa suka yi cewa mulki ya koma yankin a zaben badi: “Maganar wanda zai fito ya yi shugabancin kasar nan, PDP tana da ka’idojinta da kuma tsarin mulki na kasa.

“Kuma mu abin da mu ke bi ke nan”.