An nuna Kim Jong-un ta talabijin kai tsaye

Shugaba Kim Jong-il da dansa Kim Jong-un suna karbar gaisuwar soji
Image caption Shugaba Kim Jong-il da dansa Kim Jong-un suna karbar gaisuwar soji

Gidan talabijin na Korea ta Arewa ya nuna hotunan shugaban kasar, Kim Jong-il, yana duba wani gagarumin faretin soji tare da dan autansa, Kim Jong-un, kai tsaye.

Wannan ne dai karo na farko da aka watsa hotunan Kim Jong-un tare da mahaifin nasa kai tsaye.

Jiya Asabar ma, mutumin da ake kallo a matasayin shugaban kasar mai jiran gado ya bayyana a gaban kafofin yada labarai na duniya lokacin wasu bukukuwa a Pyongyang, babban birnin kasar.

Kim Jong-un ya tsaya ne tare da mahaifin nasa a kan wani dandamali inda suka karbi gaisuwar sojojin kasar suka kuma rika tafi yayinda makamai masu linzami, da tankokin yakin kasar ke wucewa ta gabansu.

Hakan dai ya kara jaddada matsayin dan autan shugaban na Korea, dan shekaru ashirin da bakwai da haihuwa, a rundunar sojin kasar.

A watan da ya gabata ne dai aka ba Kim Jong-un mukamin janar a rundunar da kuma wani muhimmin mukamin siyasa.

Faretin dai wani bangare ne na bukukuwan murnar cika shekaru sittin da biyar da kafa Jam'iyyar Ma'iakata ta Korea ta Arewa, to amma masu sharhi na ganin wani muhimmin mataki ne na kintsa Kim Jong-un ya karbi ragamar mulkin kasar daga hannun mahaifinsa, wanda ke fama da rashin lafiya.

Haka kuma faretin ya baiwa al'ummar kasar damar yin ido hudu da shugaban mai jiran a karo na farko.

Karin bayani