Daliban Haiti 160 za su je Senegal

Shugaban Senegal, Abdoulaye Wade
Image caption Shugaban Senegal, Abdoulaye Wade

Ana sa ran wani jirgin saman da aka yi shatarsa zai tashi daga Senegal don ya kwaso dalibai dari da sittin wadanda girgizar kasar Haiti ta shafa a watan Janairu.

Bayan bala'in girgizar kasar ne dai Shugaba Abdoulaye Wade na Senegal din ya yi alkawarin taimakawa al'ummar Haiti ta hanyar samar da filaye ga wadanda ke sha'awar yin kaura zuwa Afirka da kuma gurabe a jami'a ga dalibai.

Shugaba Abdulaye Wade ya ce ya yiwa mutanen Haiti wannan tayin ne saboda tushensu daya ne da al'ummar kasarsa.

Akasarin mutanen Haiti dai jikokin bayin da turawan mulkin mallaka suka kwasa ne daga nahiyar Afirka.

A cewar Shugaba Wade, mutanen Haiti 'yan asalin Afirka ne suna kuma da ikon sake komawa gida.

Ranar Laraba ne dai ake sa ran daliban, wadanda shugaban kasar Haiti, Rene Preval, zai yiwa rakiya, za su sauka a Dakar.

Shugaba Wade ne kuma da kansa, wanda ya bukaci iyalai a Senegal din su sama musu wurin zama, zai tarbe su.

Ko kafin girgizar kasar da ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane dubu dari biyu da ashirin da kuma salwantar da dukiyoyi masu dimbin yawa dai, Haiti ce kasar da fi talauci a arewacin duniya.

Sai dai ita ma Senegal din tana fama da irin nata matsalolin, wadanda suka hada da tsananin rashin aikin yi da kuma gajiyawar tsarin bayar da ilimi kyauta.

Bayan kakkausar suka dai Shugaba Wade ya manta da batun baiwa mutanen Haiti filaye kyauta, to amma masu adawa da shi sun ce ya fi sha'awar yin manya-manyan alkawura a kan mayar da hanakali wajen magance matsalar tattalin arzikin kasar ta Senegal.