Najeriya: Malaman jami'o'i na yajin aiki

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, yau ne malaman jami’o’i za su fara wani yajin aikin gama-gari na tsawon kwanaki uku.

Hakan ya biyo bayan umurnin da kungiyar malaman, wato ASUU, ta baiwa ’ya’yanta dake fadin kasar ne da su shiga yajin aikin don nuna goyon bayan su ga takwarorinsu da ke jami’o’in jihohi a yankin kudu maso gabashin Najeriyar.

Malaman jami’o’in jihohin wannan yankin dai sun shafe fiye da watanni biyu suna yajin aiki a kokarin ganin gwamnatocin jihohin sun yi aiki da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kungiyar ta ASUU da gwamnatin tarayya da kuma wakilan jihohin kasar a shekarar da ta gabata.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Ukachukwu Awuzie, ya ce yajin aikin tsokaci ne “don ankarar da jama'a cewa gwamnatocin wadansu jihohin ba su shiryawa tafiyar da jami’o’i ba”.

Ya kuma ce idan wannan mataki bai haifar da sakamakon da ake nema ba, majalisar zartarwar kungiyar za ta yanke shawarar matakin da ya kamata su dauka.