ECOWAS na neman mafitar tsaro a yankinta

ECOWAS na neman mafitar tsaro a yankinta
Image caption ECOWAS na neman mafitar tsaro a yankinta

Kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, watau ECOWAS ko CEDEAO, tana gudanar da wani taro a birnin Accra na kasar Ghana, a kan sha'anin tsaro a yankin.

Mahalarta taron da suka hada da manyan jami'an soja da na kwastan, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, suna ganawa ne a asirce, domin ganin yadda za a bullowa wasu matsalolinda suka addabi yammacin Afirkar, kamar safarar miyagun kwayoyi, da fataucin jama'a, da halatta kudaden haram.

Kungiyar ECOWAS, da gwamnatin Amirka da ta Ghana, su ne suka dauki nauyin taron, wanda za a kwashe mako guda ana yi.