Palasdinawa sun yi watsi da Israela

Tattaunawa ta lalace tsakanin Israela da Palasdinawa
Image caption Tattaunawa ta lalace tsakanin Israela da Palasdinawa

Jami'an Palasdinawa sun yi watsi da tayin da pira ministan Isra'ila, Benyamin Netanjahu yayi na dakatar da gine ginan matsugunan yahudawa 'yan kama wuri zauna, muddin za su dauki Isra'ila a matsayin 'yantacciyar kasa. Mr. Netanyahu yace: Kamar yadda Palasdinawa ke son mu dauki kasarsu a matsayin 'yantacciyar kasa, muma muna da 'yancin ganin sun dauki kasar Yahudawa haka.

Wani babban jami'in Palasdinawa dake cikin tattaunawar sasatawar da ake yi ya ce, ai dama sun dauki Isra'ila a matsayin kasa, babban batun dake barazana ga tattaunawar zaman lafiyar shi ne, na gine-ginan matsugannan yahudawa da suke yi wanda ya sabawa doka.

Palasdinawa dai sun janye daga tattaunawar da Amurka ta dauki nauyi ne, saboda Israela ta ki dakatar da gine ginen matsugunan Yahudawa yan kama wuri zauna.