Yar Najeriya ta yi amfani da haramtattun kwayoyi

Yar tseren Najeriya Damola Osayemi
Image caption Damola Osayemi ita ce 'yar wasa ta farko da aka samu da laifin amfani da miyagun kwayoyi a gasar ta bana

An kama 'yar tseren Najeriya Damola Osayemi, wacce ta lashe zinare a gasar mita 100 ta mata da amfani da kwayoyin da ke kara kuzari a gasar kasashen Commonwealth ta bana.

Shugaban gasar ta Commonwealth Mike Fennell, ya ce an nemi Osayemi ta gabatar da gwajin fitsarinta na biyu, sannan ta gurfana a gaban hukumar a ranar Litinin.

Yar Najeriyar mai shekaru 24, ta samu nasara ne ranar Alhamis, bayanda aka dakatar da 'yar Australia Sally Pearson.

Wannan shi ne karo na farko da aka samu wani yana amfani da kwayoyin da ke kara kuzari a gasar ta bana.

An samu 'yar tseren ne da laifin amfani da kwayar methylhexaneamine, wacce a 'yan kwanakin nan aka sanya a cikin jerin kwayoyin da aka haramta amfani da su.

Idan har aka tabbatar da gwaji na biyu, to za a baiwa 'yar kasar Ingila Katherine Endacott, wacce ta zo ta uku lambar azirfa.

A yanzu dai babu wani mataki da aka dauka game da lambar zinaren da Osayemi ta samu, har sai bayan ganawar da mahukunta za su yi da ita.