Za a warewa bangaren lafiya asusu a Zimbabwe

Shugaba Robert Mugabe da Firayim Minista Morgan Tsvangirai
Image caption Shugaba Robert Mugabe da Firayim Minista Morgan Tsvangirai

Ministan lafiya na kasar Zimababwe, Dakta Henry Madzorera, ya ce duk wani kudin da za a yi amfani da shi wajen inganta tsarin kiwon lafiyar kasar, kamata ya yi a ajiye shi a wani asusu na musaman wanda ba ya karkashin ikon gwamnatin kasar.

A hirar da yayi da BBC, Ministan ya nanata kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ga gwamntocin kasashen duniya su zuba jari da yawan su ya kai miliyoyin daloli a bagaren kiwon lafiya.

“Akwai gaskiya a bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta yi.

“Mutane da dama na mutuwa a Zimbabwe, kama daga yara da kuma mata da sauransu, sanadiyyar cututtukan da za a iya shawo kansu”, inji Ministan.