Mataimakin Darakta-Janar na BBC zai bar aiki

Mark Byford na BBC
Image caption Mark Byford ya shafe shekaru 32 yana aiki a BBC

Hukumomin BBC sun bada sanarwar cewa mataimakin Darakta-Janar, Mark Byford, zai bar aikinsa a watan Maris mai zuwa, inda kuma za a soke mukamin baki daya.

Mista Byford, wanda ya shafe shekaru fiye da 30 a BBC, albashinsa yakai fan 475,000, ana saran zai karbi tsakanin fan 800,000 ko fan 900,000 a matsayin ladan ajiye aiki.

Darakta-Janar na BBC Mark Thompson ya yabawa "juriyarsa da kuma biyayya".

A shekara ta 2007, bayan da BBC ta fuskanci matsala ta fuskar kudaden shiga daga masu kallon talabijin, ta ce za ta rage guraban ayyuka 1,800 cikin shekaru shida.

Ta kuma yi alkawarin za ta rage kudaden da take biyan manyan shugabanninta da kashi daya bisa hudu, bayanda ta sha suka a bisa dimbin kudaden da take biyan su.

'rage adadin manyan mukamai'

Mista Thompson yace: "Mark ya taka rawar gani sosai a 'yan shekarunnan a matsayinsa na shugaban ayyukan jarida na BBC baki daya, kuma ya zamo min mataimaki na kwarai.

"Sai dai a kokarinmu na kashe kudaden shigarmu kan shirye-shiryen da muke watsawa, muna duba yadda za mu rage adadin manyan mukaman da ake da su domin rage kudaden da ake kashewa."

Mista Byford, mai shekaru 52, yana da jumullar albashin da yakai fan 488,000, kamar yadda asusun BBC na shekarar 2009 da 2010 ya nuna.

Mista Byford ya zamo mataimakin Darakta-Janar ne a watan Janairun shekara ta 2004.

Wakilin BBC kan kafafan watsa labarai Torin Douglas, ya ce duk da cewa mista Byford shi ne na farko da ya bar mukaminsa, da alamu akwai da dama da za su biyo bayansa.

A wani jawabi da ya aikewa baki dayan ma'aikatan BBC, ya bayyana farin cikinsa game da shekarun da ya shafe yana aiki a BBC, tare da yi mata fatan alheri.