Mahaka ma'adinan Chile na dab da fitowa

Iyalan mahaka ma'adinai a Chile
Image caption Iyalan mahaka ma'adinai a Chile

A kasar Chile, nan da 'yan sa'o'i kalilan ne ake sa ran soma aikin ceto masu hakar ma'adinan nan talatin da ukku, wadanda sama da watanni biyu kenan suke can karkashin kasa, sun rasa na yi.

Ministan ma'adinan Chilin ya ce, a daren yau ne za a fito da mutum na farko.

Masu aikin ceton zasu kwashe awoyi arba'in da takwas suna aikin ba kakkautawa.

Za a fito da mutanen talatin da ukku daya bayan daya, a cikin wani keji na karfe na musamman da aka kera.

Shugaban kasar Chile, Sebastian Pinera, ya isa wurin hakar ma'adinan, domin ganin yadda aikin ceton zai gudana.