INEC ta ce jinkiri ka iya shafar mika mulki

Jinkiri ka iya shafar mika mulki
Image caption Jinkiri ka iya shafar mika mulki

A Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta ce duk wani jinkirin da za a iya samu, wajen yiwa dokokin zabe gyaran fuska, zai iya shafar ranar mika mulki, wato ashirin da tara ga watan Mayun badi. Hukumar ta ce, dole ne majalisar dokokin kasar ta kammala gyaran fuska ga dokokin zaben, ta yadda za a gudanar da zaben a watan Afrilun badi don gudun kada mutane su fara dari dari da hukumar.

To sai dai majalisar wakilan kasar wadda ta koma hutu a yau, ta ce sai nan gaba ne za ta yanke shawara game da batutuwan da aka gabatar mata, wadanda suka hada da tura lokacin zaben daga watan Janairu zuwa watan Afrilun badi.