Masu hakar ma'adinai a Chile sun kusa fitowa

Gwajin akurkin da za a fito da mutanen
Image caption Gwajin akurkin da za a fito da mutanen a cikinsa

Yayin da ya rage kasa da sa'o'i ashirin da hudu a fara fito da mutanen nan talatin da uku masu hakar ma'adinai a kasar Chile, zumudi sai karuwa ya ke yi a sansanin da ke daf da mahakar ma'adinan.

Ya zuwa yanzu dai 'yan jaridu daga kafofin yada labarai na duniya kusan dubu daya ne, wadanda aka baiwa izinin shaida al'amarin, ke dandazon kama wuri a dandamalin da aka tanada dominsu.

Jami'ai dai sun ce za a fara aikin fito da mutanen ne cikin daren yau Talata wayewar garin gobe Laraba.

A yau din ne kuma ake sa ran shugaban kasar ta Chile, Sebastian Pinera, zai hallara a mahakar ma'adinan, inda aka kuma tsaurara matakan tsaro.

An dai kammala shirye-shiryen fito da mutanen bayan gwajin akurkin da za a debo su a cikinsa jiya Litinin.

Sannan kuma za a sake yin wasu gwaje-gwajen kafin a zura jami'an da za su taimakawa mutum na farko ya fito duniya ta ganshi.

Dimbin dangin mutanen ne dai suka hallara a kewayen mahakar ma'adinan don yin marhabin da su.

Angelica Pina, wata mai sayar da tufafin mata, ta raba kaya ga mata da ma ’yanmatan mutanen talatin da uku don su yi kwalliyar da ta dace da tarbar mazaje da samarin nasu.

Daya daga cikin matan 'yar shekaru hamsin da bakwai da haihuwa, Lilian Ramirez, ta samu kayan amare ne, to amma a cewarta ba irin kayan da ta ke sha'awar sanyawa ba ke nan.

“Wata kyakkyawar doguwar riga zan saya da takalama masu tsinin dunduniya, sannan kuma zan je a yi min gyaran gashi”, inji Lilian.