Obama ya yiwa David Cameron ta'aziyya

 Linda Norgrove
Image caption Ma'aikaciyar agaji 'yar Burtaniya, Linda Norgrove

Shugaba Obama na Amurka ya yiwa Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron, ta'aziyya ta waya dangane da mutuwar ma'aikaciyar agajin nan 'yar Burtaniya a Afghanistan.

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta bayyana cewa Shugaba Obama ya kuma ce ayyukan da Linda Norgrove ta gudanar a Afghanistan sun nuna irin sadaukar da kai da ta yi don ci gaban rayuwar al'umma.

Shugaba Obama da Mista Cameron dai sun yi ittifaki a kan cewa yunkurin da aka yi na kubutar da ita ya wajaba ne saboda rayuwarta na cikin hadari, kuma yana da muhimmanci a binciki hakikanin abin da ya faru.

Ko da yake jim kadan bayan yunkurin kubutar da ma'aikaciyar agajin, jami'an runar NATO sun ce wadanda suka kama ta ne suka kashe ta, an samu sababbin bayanan da ke nuna cewa mai yiwuwa gurnetin sojojin Amurka ne ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Kwamandan dakarun Amurka na musamman ne dai ya bayyana yiwuwar hakan bayan ya kalli wani hoton bidiyo wanda aka dauka da na'urar daukar hoton da ke makale a hular-kwanon daya daga cikin dakarun nasa.