Ana ci gaba da zakulo mahakan ma'adinan Chile

Florencio Avalos da Shugaba Sebastian Pinera sun rungumi juna
Image caption Florencio Avalos da Shugaba Sebastian Pinera sun rungumi juna

Ya zuwa yanzu an samu nasarar fito da wasu daga cikin masu hakar ma'adinan nan talatin da uku da suka shafe fiye da watanni biyu a karkashin kasa a Chile.

Da misalin karfe goma sha biyu da 'yan mintoci na dare agogon Chile ne dai mutum na farko ya iso doron kasa yayinda mutum na biyu ya fito kusan awa guda bayan nan.

An yi ta sowa da tafi lokacin da Florencio Avalos ya fito daga cikin kejin da ya dauko shi.

Fitowarsa ke da wuya ya rungume dan karamin dansa wanda ke ta zubar da hawayen farin ciki, da kuma Shugaban Kasa Sebastian Pinera.

An dai zabi Mista Avalos ya fara fitowa ne saboda yana cikin wadanda suka fi koshin lafiya a cikin mutanen talatin da uku.

An kuma ba shi wani tabarau wanda zai kare idanuwansa daga haske mai karfi sannan aka kai shi wani wuri da aka kebe don duba wadanda aka ceto.

Bayan 'yan mintuna ne kuma Shugaba Pinera ya yi jawabi ga al'ummar kasar, yana cewa:

“Wadannan mahaka ma'adinai, kamar wadanda girgizar kasar watan Fabrairu ta shafa, sun tabbatar da cewa idan al'ummar Chile ta hada kai to za ta iya cimma abubuwan mamaki.

“Kasar nan ta nuna irin karfin halin da ta ke da shi idan ta fada cikin wani bala’i”.

Kusan awa daya bayan fitowar Mista Avalos ne dai mutum na biyu, Mario Sepulveda, ya samu fitowa, sannan kuma bayan wata awa dayar Juan Ilanes ya biyo bayansa.

Mutum na hudu da ya fito dai, Carlos Mamani, dan kasar Bolivia ne.

Jami'ai sun ce heliman mahakar ma'adinan, Luis Urzua, shi ne zai fito daga karshe a aikin ceton da suka ce zai dauki kusan sa'o'i arba'in da takwas.