Shugaban Najeriya ya amince da sayar da NITEL

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya amince a sayar da da kamfanin sadarwa na NITEL a kan kudi fiye da dala miliyan dubu biyu.

Wani hadingwiwar kamfanonin Najeriya da China da kuma kasashen Larabawa dai aka sayar wa kamfanin, an kuma bukace su su yi biya biyu.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin cewa mai yiwuwa tayin da aka yi a kan NITEL din ya sa farashin da aka sanyawa kamfanin ya wuce kima.

A farkon shekarar da muke ciki ne aka samu tsaiko a batun sayar da kamfanin, bayan binciken da gwamnatin kasar ta gudanar a kan kamfanonin da suka hada gwiwar.