EFCC ta gurfanar da na kusa da Shugaba Obasanjo

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta Najeriya, wato EFCC ta gurfanar da tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shawara, kuma tsohon babban Sakataren kasar, a gaban wata babbar kotu dake Abuja.

Hukumar ta gurfanar da Mr. Adeyanju Bodunde ne a gaban kotun bisa zargin aikata wadansu laifuka shida da suka danganci halatta kudaden haram.

Hukumar na tuhumar Mr Adeyanju ne tare da wadansu da laifin karbar wadansu kudade da suka haura Dalar Amurka Miliyan biyar a tsakanin shekarun 2002 zuwa 2003.

Wannan dai ya biyo bayan shigar da kara da ofishin Ministan Shari'a na kasa ya yi a kan kamfanin Mai zube Holdings Limited, mallakin tsohon shugaban kasar, Janar Abdulsalami Abubakar, inda yake tuhumar Mr. Adeyanju Bodunde tare da wadansu mutane 14 da karbar cin hanci.