Amurka ta tuhumi 'yan damfara

Shugaban Amurka,Barack Obama
Image caption An tuhumi 'yan damfara a Amurka

Fiye da mutane saba'in ne ake tuhuma da damfarar tsarin inshorar lafiyar Amurka.

Ana tuhumar mutanen ne, wadanda ke da tsatson kasar Armenia, da bude asibitocin bogi don karbar kudi fiye da dala miliyan 163 daga hukumar inshorar Amurkar, da zummar kula da tsoffin mutane.

Ana zargin cewa an shirya yaudarar ce a wasu jihohin Amurka ashirin da biyar.

Amurka ta ce 'yan damfarar na karkashin shugabancin wani dan kasar ta Armeniya, wanda ke tsare a gidan yarin da ke birnin Los Angeles.

Jami'an leken asirin Amurka, FBI sun kama mutane 52 ranar laraba.Kuma mutane 73 ne ake tuhuma da aikata wannan aika-aika.