Shugaban Chile yayi alkawarin fiddo sabbin dokoki

shugaba Pinera na Chile
Image caption shugaba Pinera na Chile

Shugaban kasar Chile Sebastian Pinera yayi alkawarin bullo da wasu sabbin dokoki wadanda zasu hana aukuwar irin hadarin da ya auku, wanda yayi sanadiyar binne wasu mahaka ma'adinai su talatin da uku a wata mahakar ma'adinai, na tsawon sama da watanni biyu.

Lokacin da yake jawabi, bayan ganawa da mahaka ma'adinan da aka kubutar, a wani aikin ceto mai ban al'ajabi, Mr Pinera ya ce ba za a taba bari al'umar Chile su sake yin aiki a wani yanayi mai hadari irin wannan ba, wanda babu tausayi a cikinsa.

Ya kuma bada sanarwar cewa za a sake duba dokar hakar maadinan karkashin kasa, da nufin gyara ta.

Likitocinda ake duba mahaka ma'adinan, sun ce suna cikin koshin lafiya sosai.