Galibin masu hakar ma'adinan Chile na cikin koshin lafiya

Mario Sepulveda
Image caption Mario Sepulveda

A kasar Chile, likitocin da ke duba masu hakar ma'adinan nan talatin da ukku, wadanda aka ceto bayan sun kwashe fiye da watanni biyu a karkashin kasa - sun ce abin mamaki galibinsu suna cikin koshin lafiya, kuma watakila nan gaba a yau a sallami wasunsu daga asibiti.

A cewar jami'an lafiyar, idanun yawancin masu hakar ma'adinan ba su fuskantar barazana daga hasken rana, kuma ana samun nasara a kulawar da ake basu.

Fito da mutanen daga karkashin kasa ya kasance da ban al'ajibi.

'Yan kasar ta Chile sun yi ta bayyana farin cikinsu da aikin ceton tare da nuna alfahari.

Sauran kasashen duniya kuma suka rika aikawa da fatan alheri.

Miliyoyin jama'a a sassa dabam daban na duniya sun rika kallon abubuwan da ke faruwa kai tsaye ta talabijin, ko kuma sauraro ta rediyo.