turjiyar Hezbollah ta fi karfin makaman Isra'ila

Shugaba Ahmadinejad na Iran
Image caption Shugaba Ahmadinejad na Iran

Shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad, ya shaidawa wani babban taron gangami na magoya bayan kungiyar Hezbollah a kudancin Lebanon cewa, turjiyar da Lebanon ke yi, ta fi karfin dukkan makaman Isra'ila. Jawabinda shugaban na Iran yayi a wani filin wasa a garin Bint Jbeil - inda nan ne Hezbollah ta fi karfi a kudancin Lebanon - wanda kuma bai da nisa da iyaka da Isra'ila, shine jawabi mafi mahimmancin da yayi, a ziyarar da ya kai Lebanon din.

Mahmoud Ahmadinejad ya sami kyakyawan marhabun daga dimbin jama'ar da suka taru, kuma an rika yin kade-kade na soja.

Can kuma a tsallaken iyaka, Isra'ila tayi Allah wadai da ziyarar shugaban na Iran, wadda ta ce ta tada zaune tsaye ce.