Shugaban Iran na ziyartar kudancin Lebanon

Kungiyar 'yan shi'a ta Lebanon, Hezbollah, tana tattara jama'a a kudancin Lebanon din, domin marabtar shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad, wanda zai ziyarci yankin nan gaba a yau.

Shugaban na Iran zai kai ziyara a Bint Jbeil, garin da Hezbollar ta yi kaka-gida a kudancin Lebanon din, wanda ke da tazarar kilomita kalilan daga iyaka da Isra'ila.

Isra'ilar ta kai hare hare a garin, a lokacin yakin da ta gwabza da Hezbollar a 2006.

Iran ce ta bada yawancin kudaden da aka yi amfani da su wajen sake gina garin na Bint Jbeil.