An kama wani tsohon jami'in Sojin Nijar

Janar Salou Djibo, shugaban mulkin sojan Nijar
Image caption Janar Salou Djibo, ya yi alkawarin mayar da Nijar kan tafarkin dimokradiyya

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta kama Kanal Abdoulaye Badie, wanda ya taba zama mutum na biyu mafi girman mukami a majalisar mulkin sojin kasar.

Kanal Abdoulaye Badie na daga cikin manyan shugabannin majalisar sojojin da suka yi juyin mulkin a watan Fabrerun da ya gabata.

Kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan dalilan da suka sa aka kamashi.

Kafafen yada labarai a kasar sun ce, ana zarginsa da almubazzaranci da dukiyar jama'a da kuma yunkurin kawo cikas a kokarin da akeyi na maida kasar kan tafarkin dimokradiyya.

A watan Fabreru mai zuwa ne ake saran gudanar da zaben shugaban kasa a kasar.