Nijar ta cafke ta cafke wani babban hafsa

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta dakatar da wani jami'in soja, wanda a da shine sakataren CSRD, watau hukumar koli ta mulkin soja.

Kanar Abdoulaye Badie, na daya daga cikin manyan jami'an sojan da suka kwaci mulki a watan Fabrairun da ya wuce.

Sojojin basu fito fili sun yi bayyani a kan dalilan kama shi ba.

To amma kafofin yada labarai a Nijar din sun ce, ana zargin Kanar Abdoulaye Badien da yin almubazaranci da kudaden gwamnati, da kuma kokarin yin kafar angulu ga shirin mayar da kasar bisa tafarkin demokradiyya.

A karshen watan Janairun badi ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasar ta Nijar.