Hukumomi a Najeriya na ci gaba da kokarin habbaka samar da wutar lantarki

Hukumomin Najeriya sun kaddamar da wani taron masana da masu son saka jari a fannin wutar lantari a kasar.

Taron na kwanaki biyu fadar gwamnatin Najeriya ce ta kira shi da zimmar jawo hankalin masu son saka jari a fannin, makonni shida bayan kaddamar da shirin habaka harkar samar da wutar lantarki a Najeriya.

To sai dai taron na kwanaki biyu na zuwa ne a wani mawuyacin hali ga jama'ar kasa, da ma masana'antunta.