Yunkurin gyara lantarki a Najeriya

Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na cikin kwamitin samar da wuta a lokacin mulkin marigayi Yar'adua

Hukumomin Najeriya sun kaddamar da wani taron masana da masu fada aji da kuma masu son saka jari a fannin wutar lantari a kasar.

Taron na kwanaki biyu fadar gwamnatin Nijeriya ce ta kira shi da zimmar jawo hankalin masu son saka jari a fannin makonni shida bayan kaddamar da taswirar habaka harkar samar da lantarki a Nijeriya.

Editan mu na Abuja Amed Idris, ya ce taron na kwanaki biyu na zuwa ne a wani mawuyacin hali ga jama'ar kasar da ma masana'antun ta.

Shi dai taron na yau da shi kan shi shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar na zuwa ne daidai lokacin da alkaluma ke nuna irin mawuyacin hali da harkokin rayuwa da tattalin arziki suka shiga ne a Nijeriya.

A yanzu haka alkaluma na nuna cewa kasar na samar da megawatts dubu uku da doriya ne na wutar lantarki ga jama'ar da yawansu ya zarta miliyan 140.

Abin da ke nuna cewa akasarin al'ummmar kasar ba su samun ta, kana a inda ake samun, wutar bata wadata ba.

Babban bankin Najeriya

Alkaluman babban bankin Nijeriya na baya bayan nan kan wutar lantarkin na nuna cewa a duk shekara ana kashewa injunan samar da wuta na 'janareta' kimanin dala miliyan dubu 13 wajen mai da gyara.

Hakan na nufi kenan kudin da ake kashewa janareta a kasar ya zarta kayaki da a ayukan da ake samarwa a cikin gida da kimanin kashi 40%.

Alhali kuwa abin da fannin wutar lantarkin Nijeriya ke bukata a duk shekara shi ne dala miliyan dubu goma na wasu 'yan shekaru kafin fannin ya mike.

Wannan a fadin shugaban kasar Goodluck Jonathan abu ne dake ciwa gwamnati tuwo a kwarya. To ko me za su yi?

Yace: "burin gwamnati ne ta tabbatar da ganin harkar samar da wutar lantarki da ita kan ta wutar sun kankama cikin dan kankanen lokaci. Don haka ne ma gwamnati ta kaddamar da taswirar wadata kasa da hasken lantarki misalin kwanaki 40 da suka gabata."

'durkushewar masana'antu'

Binciken bankin duniya dai na nuna cewa akasari 'yan Nijeriya ba su damu da karin kudi da za'a yiwa wutar ba matukar ta wadata kuma hakan bai wuce kima ba.

Wakilinmu ya kara da cewa rashin wadatar wutar ya durkusar da masana'antu, matsalar rashin aiki ta karu, kai har ma da fatara.

Shekaru sama da goma da dawowar mulkin dimokuradiya kana da dubban miliyoyin da gwamnatocin jiya da yau suka narka a harkar samar da wutar, har yanzu an kasa kai gaci saboda yadda cin hanci da sakaci suka dabaibaye al'amarin.

Har yanzu akwai manyan jami'ai na gwamnati da na majalisa da ake yiwa shari'a bisa zargin sama da fadi da kudaden harkar lantarki a kasar.

Ko da yake shugaba Goodluck Jonathan ya fadi a jawabin sa na bude taron cewa za'a kamanta gaskiya a gyaran da ake yiwa harkar lantarki a Nijeriya, da yawa cikin 'yan kasar za su jira ne su ga yadda za ta kaya, saboda alkawuran da aka yi a baya ma ba a kai ga cika su ba.