Nijar:Yawan mutuwar mata na ciwa hukumomi tuwo-a-kwarya

Mata a jamhuriyar Nijar
Image caption Mutuwar mata lokacin haihuwa na ciwa hukumomi tuwo-a-kwarya

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ce, yawan mace-macen mata wajen haihuwa na cikin matsalolin da ke ci gaba da ciwa hukumomin lafiyar kasar tuwo a kwarya.

Hukumomi dai na cewa, rashin samun tazarar haihuwa, da rashin zuwa awon ciki akai-akai na daga cikin matsalolin da ke jawo yawan mace macen matan.

Dakta Lawwali Aisa Abdu, wata likita ce, kuma ta shaidawa BBC cewa:''Mace ta dauki ciki bara,ba ta samu ta huta ba-ta yadda jikinta zai murmure, sai kuma bana ta sake dauka, hakan na yin lahani ga rayuwar ta,da ta dan da ke cikinta''

Sai dai hukumomi sun ce suna daukar matakan inganta rayuwar mata masu juna-biyu.

Dakta Yaro Asma Gali, jami'ar lafiya ce a ofishin Ministan kiwon lafiya,ta ce :''Akwai likitoci(asibitoci), wadanda a ke kara ginawa a kusa da inda mata masu junya-biyu su ke, domin kula da lafiyarsu.Kana an daina biyan kudi wajen awon ciki.Hakan zai sa su(matan) zuwa asibiti''.