Babban bankin Amurka na duba sabbin matakan zaburadda tattalin arziki

Shugaban babban bankin Amirka, Ben Bernanke, ya bada alama mafi girma kawo yanzu, cewa mai yiwuwa ya kara daukar matakan tallafawa tattalin arzikin kasar, domin ya cigaba da murmurewa.

Mista Bernanke ya ce, karuwar marasa aikin yi, da kuma hauhawar farashin kayayakin da bata taka kara ta karya ba, na ci gaba da yin barazana ga farfadowar tattalin arzikin Amirkar. Ya ce, rashin aikin yi na dogon lokaci, zai yi tasiri a kan yawan kudaden da jama'a ke kashewa, wanda hakan kuma zai shafi murmurewar tattalin arzikin.

Shugaban babban bankin Amirkan ya nuna cewa, watakila bankin ya kara saka kudade, ta hanyar sayen takardun bashi a kasuwanni.

A bangare daya kuma, sakataren baitulmalin Amirkan, Timothy Geithner, ya ce a zahiri gibin kasafin kudin kasar ya ragu a shekara kudin da ta wuce.