Babbar jam'iyar China na gudanar da taro

Shugabannin jam'iar Communist ta China
Image caption Babbar jam'iyyar China na gudanar da taro

Jam'iyar Komunisanci da ke mulki a kasar Sin, ta fara taronta na shekara-shekara ranar juma'a, inda za ta tattauna kan matsalolin koma bayan tattalin arziki da suka zame mata manyan kalubale.

Yawanci dai ana gudanar da irin wanna taro ne cikin sirri.

Sai dai a wannan karo ana gudanar da shi ne a bayyane saboda shugabannin na so masu amfani da kayayyaki su sayi kayayyakin da aka sarrafa a kasar da dama,a matsayin wata hanyar habaka tattalin arziki.

Kasar dai ta samu gagarumin ci gaban tattalin arziki a 'yan shekarun da suka gabata,sai dai yawanci hakan ta faru ne sakamakon sayar da kayayyakin ga kasashen waje.

Jam'iya mai mulkin kasar na son ta rage wagegen gibin da ke tsakanin masu hali da talakawa.