Babu wani hafsan soja da aka kama a Niger - In ji Salou Djibo

Salou Djibo
Image caption Salou Djibo

Shugaban gwamnatin mulkin sojin jamhuriyar Nijar, Janar Salou Djibo, ya shaidawa wata tawaga jami'an kungiyar Ecowas cewar babu wani jamiin soja da aka kama a kasar.

Shugaban na Niger ya shaidawa tawagar hadin gwiwa ce tsakanin tarayyar Africa da Majalisar dinkin duniya da kuma kawancen raya tattalin arzikin kasashen yammacin Africa watau Ecowas ko Cedao a lokacin wata ganawa da yayi da su ya a Niamey.

A 'yan kwanakin da suka gabata dai wasu majiyoyi sun bayyana cewar an kame wasu sojoji da suka hada da tsohon sakataren majalisar koli ta mulkin soja watau CRSD, Abdulaye Badie.

To saidai Janar Salou Djibo ya shaidawa tawagar, wadda ta isa Niger domin bin diddigin abun da ke faruwa cewar wannan magana jita-jita ce.