PDP ta bayyana bacin-ranta

Shugaban jam'iyar PDP,Chief Okwesilieze Nwodo
Image caption PDP ta bayyana bacin ranta

A Najeriya, jam'iyyar PDP ta damu da yadda yakin neman zabe a tsakanin manyan masu neman takarar shugabancin kasar a karkashinta, ya rikide zuwa na kabilanci da bangaranci.

Shugaban jam'iyar Chief Okwesilieze Nwodo ya ce,manyan masu neman takarar sun daina kamfe kan ayyukan da su ke son yiwa 'yan kasar idan a ka zabe su a matakin shugabanci.

Ya ce don haka ne jam'iyar ta gayyaci daraktocin kamfe din 'yan takarar, da zummar jan-kunnensu ta yadda za su daina kalaman batanci ga junansu.

'sabon babin siyasa'

Tuni masu lura da al'amuran siyasa a kasar ke ganin irin abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar ta PDP, musamman wajen yakin neman zabe, na neman bude wani sabon babi ne a siyasar kasar.

Sun ce matukar ba a dauki mataki kan batun ba, zai iya haifar da gagarumin koma-baya ga mulkin dimukradiya.

Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyar siyasa ne, ya shaidawa BBC cewa:''kowane dan takara na nuna bangaren da ya fito, da kuma ci gaban da bangaren zai samu idan shi(mutumin) ya hau kan mulki.