An tsaurara tsaro a Bauchi

Taswirar Najeriya
Image caption Ana ci gaba da tsaurara tsaro a Bauchi

A Najeriya, hukumomi a jihar Bauchi na ci gaba da tsaurara matakan tsaro sakamakon hare-haren da 'yan bindiga a kan babur ke kai wa jami'an tsaro.

Mataki na baya-bayan nan da hukumomin suka dauka shi ne na haramta sana'ar acaba da daddare.

Malam Abdulmumini Kundak shi ke baiwa gwamnan jihar shawara a fannin siyasa, kuma ya shaidawa BBC cewa:''Ana nan ana addu'a da bincike domin Allah ya kawo sauki''.

Ya kara da cewa a shirye gwamnati ta ke ta sasanta da masu kai hare-haren.

Sai dai har yanzu rundunar 'yan sandan jihar ta yi gum da bakinta dangane da wadannan hare-hare.