Amurka ta jinkirta wallafa wani rahoto kan kasar Sin

Sakataren Baital-malin Amurka,Tim Geithner
Image caption Amurka ta yi amai ta lashe

Amurka ta jinkirta wallafa wani rahoto da a ke ganin zai soki kasar Sin, saboda yin coge ga kudin kasar don cin gajiya wajen hada-hadar kasuwanci.

A maimokon wallafa rahoton, Washington ta jinjinawa matakan da Beijin ta dauka a cikin watan jiya, na ba da damar daga darajar kudin ta.

Sakataren baitul-malin Amurka, Tim Geithner ya ce yana da matukar muhimmanci sababbin tsare-tsaren na kasar Sin su dore.

Ana dai ganin cewa jinkirta wallafa rahoton da Amurka ta yi wani mataki ne na kaucewa cacar-baki ta fuskar kasuwanci da kasar China.

Kasar Sin dai ta rika sarayar da kudinta, abinda ya ke bata damar yiwa kasar Amurka, da sauran kasashen duniya fintinkau wajen bunkasar tattalin arziki.