Mahaka ma'adanan da aka ceto sun yi addu'o'i

Mahaka Ma'adanai a Chile
Image caption Mahaka Ma'adanai a Chile

Mahaka ma'adanai kimanin goma sha biyu ne wadanda aka ceto daga mahakar Sam Jose, suka halarci wani taron addu'o'i na musamman da aka yi a mahakar.

An yi wannan taron addu'o'i ne domin nuna godiya ga Allah ga dawowar su doron kasa cikin koshin lafiya.

'Yan uwa da abokan arziki sun hadu da mahaka ma'adanan cikin wani tanti domin gudanar da addu'o'in.

Sai dai wasu masu zanga-zanga sun yi amfani da wannan dama ta taruwar kafafen yada labarai domin nuna fushinsu ga gwamnati.

Jama'ar da suka tarun domin nuna fushinsu, su ma mahaka ma'adanai ne, amma basa cikin talatin da ukun da kasa ta rufta da su.

Sun yi korafin cewa ba a gayyace su zuwa wadannan addu'oi ba, sannan tun da aka rufe mahakar ta San Jose watanni biyu da suka wuce, ba a biya su albashinsu ba.