An fara jigilar maniyyata a Nigeria

Masjidul Haram
Image caption Masjidul Haram

A Nigeria an fara jigilar rukunin farko na maniyyata aikin Hajjin bana. Rukunin farko sun tashi daga jihohin Lagos, da Katsina da Yola da Maiduguri da kuma Ilorin.

Maniyyata akalla 500 da suka fito daga jihar Ogun a yankin kudu maso yammacin Nigeria ne suka tashi daga filin saukar jiragen sama na birnin Ikko.

Hukumomin alhazai sun ce suna sa ran jumlar maniyyatta dubu 95 ne daga Nigeria zasu sauke faralinsu a wannan shekarar.

Shugaban tawagar Alhazai na wannan shekarar, Sarkin Musulmi, Sultan Mohammed Sa'ad Abubakar, ya gargadi maniyyatan da su nuna kyakkyawar halayya a kasa mai tsarki, tare da yin tsumi da tattali akan guzurinsu.