Mutane 22 sun rasu sakamakon hari a Karachi

Akalla mutane ashirin da biyu sun rasa rayukansu a cibiyar kasuwanci ta Pakistan wato Karachi.

Hakan ta faru ne sakamakon wani hari da ake gani yana da alaka da siyasa, dab da fara gudanar da wani zabe a yau.

Bangarori daban daban masu alaka da kungiyoyin siyasa suna cigaba da kaddamar da hare-hare.

Jama'a sun bayyana damuwarsu kan abinda ke faruwa.

A cewar Imran Ahmad, wani mazaunin garin, akwai zabuka a yau, amma ala'mura sun dagule tun jiya.

An dai fara kada kuri'a na wata kujerar majalisa a lardin da shugaban MQM, Reza Haider ke rike da ita.

Rikicin da aka shiga a baya-bayan nan ya biyo bayan kauracewa zaben da jam'iyyar Awami National Party ta ce ta yi ne.