Zanga-zanga na kara kamari a Faransa

Zanga-zanga na kara kamari a Faransa
Image caption Yajin aikin ya haifar da cunkoson mai yawa a titunan kasar

Direbobin manyan motoci a Faransa sun toshe hanyoyi yayinda zanga zanga game da sauye sauyen kudaden fansho ta kara kamari, bayanda Pirayim Minista ya lashi takobin hana kanfar mai.

A yanzu shugaba Sarkozy ya kafa kwamitin gaggawa na ministoci domin shawo kan lamarin, bayanda gidajen mai suka fara fuskantar karancin man fetur.

Masu manyan motocin sun kawo cunkoson ababen hawa a kan titunan dake kusa da Paris da kuma birane da yawa na larduna.

Sannan suka toshe hanyar kaiwa ga depo - depon samar da kayayyaki sannan ma'aikatan mai na toshe matattarar mai domin kare 'yancinsu na yin ritaya a shekaru 60.

Rahotanni na nuna cewa wasu dalibai sun yi artabu da jami'an 'yan sanda a titunan birnin Lyon.

Wani malami da aka kona wa mota ya ce daliban da suka gudanar da wannan abu basu fahimci abun da ke faruwa ba.

Kasuwanin kasar dai sun fara nuna kosawar su wajen ganin cewa kasar ta shawo kan matsalar gibi da take fusknta.

Sai dai kuma kwanakin nani masu zuwa za su sa Shugaba Nicolas Sarkozy a tsaka mai wuya dangane da matakin da zai dauka.