Iran za ta shiga cikin tattaunawa kan Afghanistan

A karon farko Iran za ta shiga cikin tattaunawar da ake kan yanayin sha'anin tsaro a Afghanistan, wanda za'ai wannan makon a Rome.

Taron ya hada da manyan jami'an Amurka, Afghanistan da na NATO.

Wakilin Amurka na musamman a Afghanistan da Pakistan, Richard Hoolbroke, ya ce ya kamata a san cewa Iran na da rawar da za ta taka wajen warware rikicin da ake.

A baya jami'an Iran da na Amurka sunce za su iya aiki tare domin kawo zaman lafiya a Afghanistan.