Guguwa tafe da ruwa ta aukawa Philippines

Inda guguwar ta ratsa a Philippines
Image caption Inda guguwar ta ratsa a Philippines

An fara jin radadin wata guguwa wadda ke tafe da ruwan sama mai karfin gaske a yankin arewa maso yammacin kasar Philippines, kuma tuni har wani masunci ya mutu sakamakon nutsewa a ckin ruwa saboda karfin iskar.

Guguwar, wadda ba a taba ganin irinta ba, ta zo ne da ruwan sama kamar da bakin kwarya, da kuma iska mai karfi wadda ta shafi yankin arewacin kasar mai samar da shinkafar da ake nomawa a kasar.

Tuni dai mazauna wannan yanki suka tsere daga muhallinsu; aka kuma rufe makarantu, kana aka haramta safara ta ruwa, kuma dubban soja da masu aikin sa kai sun shiga shirin ko-ta-kwana, domin kai dauki.

Ko da a bara dai wata guguwar mai tafe da ruwa ta hallaka mutane akalla dari biyu da hamsin a kasar ta Philippines.