Gyaran tsarin mulki a Majalisar Dattawa

Harabar Majalisar dokokin Nijeriya
Image caption Harabar Majalisar dokokin Nijeriya

Majalisar Dattawan Nijeriya ta gudanar da wani taron jin ra'ayin jama'a game da aikin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar a karo na biyu.

Hukumar zaben Najeriya INEC da wasu kungiyoyi ciki da kuma jamiyyun siyasar kasar ne dai suka halarci taron jin ba'asin jama'ar.

Majalisar dattawan dai ta jaddada cewar babu gudu ba ja da baya dangane da batun rantsar da sabuwar gwamnati a ranar ashirin da tara ga watan Mayu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.