Zanga-zanga ta tsananta a Faransa

Masu zanga-zanga na kona tayoyi
Image caption Masu zanga-zanga na kona tayoyi

Yayinda Majalisar Dattawan kasar Faransa ke haramar kada kuri'a a kan sabon tsarin fanshon da Shugaba Nicholas Sarkozy ya bullo da shi a wannan makon, ana sa ran zanga-zangar ma'aikata don nuna kin jinin shirin za ta kara tsananta a yau.

Ma'aikata sun shirya yin zanga-zanga a fadin kasar ta Faransa a karo na shida cikin kasa da watanni biyu don nuna rashin amincewa da shirin na kara shekarun yin ritaya daga sittin zuwa sittin da biyu.

Tsawaitar zanga-zangar hade da yajin aiki dai ta jefa kasar cikin matsanancin karancin man fetur, inda rahotanni ke bayyana cewa daruruwan gidajen mai ba su da man ko dis, yayin da mutane ke rububin sayensa.

Ma'aikatan mai da direbobi masu yajin aiki dai sun rufe matatun man kasar tun kusan mako guda da ya wuce.

A wadansu wurare kuma an samu tashe-tashen hankula inda 'yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa a kan matasa masu fashe-fashe da kuma kona motoci.

Sai dai Shugaba Sarkozy ya ce babu gudu ba ja baya a yunkurin da ya ke yi na yin garambawul ga tsarin fansho na kasar—hakan kuma a cewarsa ya zama wajibi.