An kame tan dari na tabar wiwi a Mexico

Shugaba Felipe Calderon
Image caption Shugaba Felipe Calderon na Mexico

Sojojin Mexico sun kwace tan dari da biyar na tabar wiwi a kusa da kan iyakar kasar da Amurka.

Ba a samu nasarar kwace tabar wiwi mai yawan haka ba a cikin shekaru da dama.

Sojoji dauke da manyan makamai ne dai suka yi dirar mikiya a kan wadansu gidaje da ke wata unguwar marasa galihu a garin Tijuana, wanda ke tsallaken iyaka daga Jihar California ta Amurka.

Yayin samamen an jikkata mutum guda yayin musayar wuta, sannan kuma aka kame mutane goma sha daya.

Sojojin sun ce sun samu kunshin tabar wiwin da dama, an kuma likawa ko wanne kunshi alamar da ke nuna dillalin da za a kaiwa ita a Amurka.

Hukumomin Mexico sun ce farashin tabar wiwin zai kai dala miliyan dari uku da talatin da biyar a Mexico, amma in aka kai ta Amurka farashin zai ninka haka sau uku.