Malaman Jami'a a Nijar na korafi.

Kungiyar malaman jami'ar Abdoul Moumouni Dioffo ta Yamai, watau SNECS ta bukaci ministan Ilimi mai zurfi na kasar, Dokta Mahamane Laouali Danda da yayi murabus.

Malaman suna zargin ministan ne da kawo wasu sauye-sauyen da za su takura masu.

Kungiyar ta SNECS ta kuma yi kira ga shugaban mulkin sojan kasar, Janar Salou Djibo, da ya soke dukkan ayoyin dokar da suka kai ga kirkiro jami'o'i a biranen Zinder, da Tahoua da kuma Maradi.