Sabon tsarin labaran BBC ta wayar salula

Steve Martin
Image caption Shugaban sashin kasuwanci na BBC Steve Martin

A Najeriya, BBC ta kaddamar da wani sabon shiri wanda zai baiwa masu saurarenta a Najeriya da ke amfani da layin wayar salula na MTN, damar samun labarai ta sakon text kai tsaye ta wayoyinsu na salula.

Shirin wanda aka kaddamar a wajen bikin baja kolin kayayyakin yada labarai na kasashen Afrika, wanda ake yi wa lakabi da Africast, wanda ake gudanarwa a Abuja.

Shi dai wannan sabon tsarin na daga cikin jerin sabbin tsare-tsare na gabatar da labarai ga masu sauraro ne, irinsu sharhin kwallon wasannin Premier cikin harshen Hausa.

Wanda sashin Hausa na BBC ke gabatarwa a kowacce ranar Asabar a shirinsa na rana.

Image caption Shugabar sashin Hausa na BBC Jamilah Tangaza tana jawabi a wajen taron

Da yake bayani a wurin kaddamar da shirin, shugaban sashin kula da kasuwanci na BBC Steve Martin, ya ce BBC ta bullo da shirin ne domin saukakawa masu saurarenta damar samun labarai ta hanyoyi da daban-daban da ke tafiya da zamani.

Shugabar sashin Hausa na BBC Jamilah Tangaza, ta ce shirin na hadin guiwa ne tsakanin BBC da kamfanin MTN.

Wanda zai baiwa jama'a damar samun labaran BBC ta sakon text ta wayoyinsu na salula, da suka hada da labaran yau da kullum da wasanni da kuma labaran BBCbaki daya, amma a harshen Turanci.

Ta kara da cewa nan gaba kadan za a kaddamar da makamancin sa na harshen Hausa.

'BBC ba ta cajar kudi'

Wakilin kamfanin MTN a wajen taron Malam Shehu Abubakar, ya ce naira dari za a caji mutum a kowanne mako domin samun wadannan bayanai.

Yace duk da cewa adadin labaran da mutum zai iya samu ya danganta da yanayi zuwa yanayi, amma za su iya kaiwa dari ko fiye da haka a mako guda.

Sai dai Jamilah Tangaza ta jaddada cewa wadannan kudaden, ba BBC ce take cajar su ba, a a kamfanin wayar salulan ne ke cajar su.

Ita BBC tana samar da labaran ne kyauta.

An kasa labaran da mutane za su iya samu zuwa kashi hudu, wadanda suka kunshi labarai na yau da kullum da labaran wasanni da kuma bayanai kan kungiyar kwallon kafar da mutum yake goyon baya a gasar Premier Ingila, sai kuma labaran BBC baki daya.

Duk kalar labaran da mutum ke bukata zai aika sakon text ne tare da rubuta samfurin labarin da yake so zuwa lambar 4 2 0 0.

Wato ga misali idan mutum yana son labaran kulob din da ya fi sha'awa, sai ya rubuta sunan kulob din a sakon text, ya aika zuwa ga lamba 4 2 0 0.