An kashe wani dan sanda a Maiduguri

Hari a ofishin 'yan sanda a Maiduguri
Image caption Hari a ofishin 'yan sanda a Maiduguri

A Najeriya an kara hallaka wani dan sanda a Maiduguri. Lamarin ya faru a daren jiya ne, kuma wani dan sandan ya jikkata.

Kawo yanzu ba wanda ya ce shi ke da alhakin kisan. To amma a baya bayan nan 'yan kungiyar Boko Haram sun yi ikirarin kai hare-hare a kan jami'an tsaro da kuma shugabannin al'ummomi a jahar ta Borno.

Kusan 'yan sanda goma ne aka hallaka a wannan jahar tun daga watan Yulin da ya wuce.

Jami'an tsaro a jahar sun ce suna bullo da sabbin dubarun murkushe 'yan sari-ka-noken.