CIA ta ce ba ta yi binciken da ya dace ba

Tambarin hukumar CIA
Image caption Tambarin hukumar leken asiri ta CIA

Hukumar leken asiri ta Amurka, CIA, ta amsa cewa hakika ba ta yi binciken da ya kamata ba a kan mai nemo mata bayanan nan da ya kashe ma'aikatan hukumar bakwai bara a gashin Afghanistan.

Wani binciken cikin gida da hukumar ta CIA ta yi ya nuna cewa sakacin da aka yi ta fuskoki da dama ne ya baiwa mutumin damar kai harin.

Shi dai dan kunar bakin waken da hukumar ta CIA ta dauka aiki, mai suna Humam Khalil Al-Balawi, dan kasar Jordan ne.

Ya kuma yi ikirarin cewa ya san inda mataimakin shugaban kungiyar Al-Qa’ida yake.