Majalisar dattijan Nijeriya ta yi watsi da bukatar shugaban kasa

Goodluck Jonathan
Image caption Goodluck Jonathan

A Najeriya majalisar dattijjan kasar ta cigaba da mahawara akan bukatar shugaban kasar na yin wasu sauye sauye akan dokar zaben 2010, inda taki amincewa da bukatar shugaba Goodluck Jonathan na saka ministocinsa da wasu manyan jami'an gwamnati a matsayin masu fidda 'yan takara wato 'delegates'.

Bayan zazzafar mahawara dai, 'yan majalisar da gaggarumin rinjaye suka ki amincewa da wannan bukatar.