Jirgin ruwa dauke da guba ya bata a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce, wani jirgin ruwan daukar kaya da ake tsare dashi a tashar ruwan Tincan Island dake Lagos, yayi sama ko kasa.

Jirgin ya bar kwantenoni bakwai a baya, wadanda ake zargi su na dauke da wadansu sinadarai da ka iya barazana ga rayuwar bil'adama.

Hukumar da ke tabbatar da kare muhalli ta kasar, NESREA, ta bayyana cewa jirgin ruwan mallakin Birtaniya, wanda ke dauke da mafi yawan kayan da wa'adin moruwarsu ya kare, ya bar tashar jirgin ruwan ne ba tare da sanin ta ba.

Hukumar NESREA ta bayyana cewa, jirgin ruwan mai suna Grand America, ya jibge kwantenoni tun kafin ta kammala bincike akan kayan.

A lokutan baya ma NESREA ta ci tarar wani jirgin ruwan mai suna VERA D, wanda ke dauke da kaya makamantan wannan.